Posts

Showing posts from January, 2018

YADDA AKE KIRKIRAR GROUP LINK A DANDALIN WHATSAPP

Image
      Sanin kowa ne musamman masu amfani da dandalin whatsapp cewar, Whatsapp group zaure ne da ake amfani dashi domin tattaro mabanbantan mutane daga mabanbantan wurare, da zummar kasancewa awuri daya domin tattauna babutuwan da ake bukatar tattaunawa. Wadan su zaurukan  suna kasancewa ne na abokai zalla, wasu kuma na addini, wasu na siyasa, wadansu kuma abokan karaatu ne kawai ke acikin shi. Wadan su mutanen kuwa,kan kirkira zaurukan whatsapp ne amatsayin Aji na daukarkar darassu awani daga cikin bangare na Ilimi, musamman ga masu koyo da koyarwa a yanar gizo wato E-Learning. Whatsapp group yanada tsari kamar sauran zaurukan sada zumunta, a inda ya kasance akwai ADMIN wato mai kula da zauren, Shine yake da damar sakawa ko cire mutum a wannan zaure. wani ko wata ba zai iya zamowa member a wannan group din ba, har sai ya mika bukatar hakan zuwa ga admin sannan admin ya almunce masa ya saka shi awan nan group din. Akwai lokacin da mutum ke son Gayyata...