YADDA AKE KIRKIRAR GROUP LINK A DANDALIN WHATSAPP
Sanin kowa ne musamman masu amfani da dandalin whatsapp cewar, Whatsapp group zaure ne da ake amfani dashi domin tattaro mabanbantan mutane daga mabanbantan wurare, da zummar kasancewa awuri daya domin tattauna babutuwan da ake bukatar tattaunawa. Wadan su zaurukan suna kasancewa ne na abokai zalla,
wasu kuma na addini, wasu na siyasa, wadansu kuma abokan karaatu ne kawai ke acikin shi. Wadan su mutanen kuwa,kan kirkira zaurukan whatsapp ne amatsayin Aji na daukarkar darassu awani daga cikin bangare na Ilimi, musamman ga masu koyo da koyarwa a yanar gizo wato E-Learning.
Whatsapp group yanada tsari kamar sauran zaurukan sada zumunta, a inda ya kasance akwai ADMINwato
mai kula da zauren, Shine yake da damar sakawa ko cire mutum a wannan zaure. wani ko wata ba zai iya zamowa
member a wannan group din ba, har sai ya mika bukatar hakan zuwa ga admin sannan admin ya almunce masa ya
saka shi awan nan group din. Akwai lokacin da mutum ke son Gayyatar mutane zuwa ga zauren sa na whatsapp, sai ya kasance dole sai ya rarraba lambar wayarsa ga mutane wadda ya ke whatsapp da ita, baya da haka sai ya aiko masa da bukatar hakan sannan ne zai iya saka shi a group din. Gaskiya yin hakan kan dauki dan lokaci. Domin zaka iya samun lambar
ne yayin da kake surfing da browser, kaga kuwa sai kayo copy sannan kazo dialling screen kayi paste, sannan kayi adding dinta acontact kayo seaching awhatsapp, kana kayi mashi sako sannan ne idan yayi add din ka zaka samu shiga.
To a irin wannan halinne whatsapp suka kirkiro WHATSAPP GROUP LINK, inda zasu baka link address wanda
da zarar mutun yayi click akan sa zai kaika gamida da saka acikin group din. Ana amfani da wanne ne idan group din ya kasance open group, idan kuwa nasu mutane ne na musamman, sai ka baiwa wadanda kake son su a group
YADDA AKE SAMUN SA:
1. kirkirar group a farko
2. sai kaje group info
3. Add participants
4. Invite to group via link.
Zaka sun baka link kamar haka: http://chat.whatsapp.co/h786jnfvduerv8u568h8.
sai kayi copy din shi. shine link din ka na group din, sai kacigaba da sharing din sa. Bugu da kari, kuma kana iya canza wannan link din idan yayi maka tsawo, zuwa kadan kamar goo.gl/Pu6lf. Domin yin munada kasida ta musamman. Kasance damu a shafin mu Amarawa Online
ko a Whatsapp
Ko a Facebook
Comments
Post a Comment