Amfanin Google Drive
YAYA AKE AMFANI DA GOOGLE DRIVE? MENENE GOOGLE DRIVE? Google Drive wata ma'adana ce , wadda kamfanin Google ya kirkirota a aranar ashirin da hudu da watan afrilun dubu biyu da sha biyu 24 April, 2012. Kamfanin na Google ya kirkiro wannan ma'ajiyar ce domin ya baiwa abokan huddarsa damar dorawa da saukewa, ajiya da kuma rarraba kayayyakin su, wadanda suka shafi bayanai da kayayyaki irin na na'urorin wayoyi da kwamfiyuta (files da softwares), wadanda da suka kunshi; hotuna, hotunan bidiyo, sautuka na murya, manhajoyin wayoyi da kwamfiyotoci, a jikin uwar garken kamfanin na google wato Google server kuma a kyauta. Wannan kusan ace itace dama ta farko da wani kamfanin yanar gizo ya taba baiwa masu hulda da shi atsawon tarihi, kasancewar dukkan wani mai ta'ammali da kafar sadarwar yanar gizo ya san makudan kudin da mutan kan biya, domin adana masa bayanan sa a yanar ta gizo, musamman bayanai masu nauyi. Ana cikin wannan halin ne Google ya kawo wannan garabasa, inda y...