Amfanin Google Drive

YAYA AKE AMFANI DA GOOGLE DRIVE?
MENENE GOOGLE DRIVE? Google Drive wata ma'adana ce , wadda kamfanin Google ya kirkirota a aranar ashirin da hudu da watan afrilun dubu biyu da sha biyu 24 April, 2012. Kamfanin na Google ya kirkiro wannan ma'ajiyar ce domin ya baiwa abokan huddarsa damar dorawa da saukewa, ajiya da kuma rarraba kayayyakin su, wadanda suka shafi bayanai da kayayyaki irin na na'urorin wayoyi da kwamfiyuta (files da softwares), wadanda da suka kunshi; hotuna, hotunan bidiyo, sautuka na murya, manhajoyin wayoyi da kwamfiyotoci, a jikin uwar garken kamfanin na google wato Google server kuma a kyauta. Wannan kusan ace itace dama ta farko da wani kamfanin yanar gizo ya taba baiwa masu hulda da shi atsawon tarihi, kasancewar dukkan wani mai ta'ammali da kafar sadarwar yanar gizo ya san makudan kudin da mutan kan biya, domin adana masa bayanan sa a yanar ta gizo, musamman bayanai masu nauyi. Ana cikin wannan halin ne Google ya kawo wannan garabasa, inda yake baiwa dukkan mutum daya katon wurin ajiyar da yakai girman 15,000. Megabyte, wato megabyte dai-dai har dubu goma sha biyar Gigabyte shabiyar kenan 15 gigabyte akyauta babu ko sisi.
DA WACE IRIN WAYA KO KWAMFIYUTA ZAN IYA AMFANI DA GOOGLE DRIVE? Tabbas ana iya amfani da Google Drive a kwamfiyuta babba ko karama, wacce take amfani da Operating System na Windows OS, ko Mac OS. Haka kuma masu amfani da wayoyin tafi da gidan ka da na'urar tablet na android ma'damar android version din ya kai 4.1 Jelly Beans zuwa abunda yayi sama nada damar amfani da wannan application din. Sauran wayoyin iPhones da iPad ma ba'a manta da su ba, domin suma suna da damar amfani da shi.
A INA NE ZANI IYA SAMUN GOOGLE DRIVE Ga dukkan mai bukatar samun wannan application din na google drive, sai ya garzaya zuwa shafin su na internet a http://www.drive.google.com domin downloading din sa, haka kuma wasu daga cikin wayoyin android suna zuwa da shi, kuma ma masu amfani da android zasu same shi a Google play store.
YADDA AKE BUDE GOOGLE DRIVE Ga dukkan maibukatar amfani dashi, to ya tabbatar da cewar yanada da account na google, wato gmail account. idan babu to sai mutum ya garzaya zuwa http://www.gmail.com domin budewa, gomin kuwa mutm na shiga Google drive din zasu fara ne da tambayarka gmail account din.
KARIN BAYANI DAN GANE DA GOOGLE DRIVE Kar amanta da cewar manufar kirkiro wannan applicion itace domin abaiwa mutane damar adanawa da rarraba files din su ayanar gizo, kuma idan wannan memory din da aka baiwa mutum damar ajiya acikin sa na kyauta wato 15gigabyte yayi masa kadan, to yana da damar fadada shi wato ya karashi, amma fa zai rinka biyan filin daya kara akan wa'adin wata wata ko shekara shekara. Ga farashin nan: 100GB =$19.99 ashekara, 1000GB =$99.99 ashekara, 2000GB =$19.99 awata. da dai sau ransu.
kasance damu a Amarawa Online ko a Facebook ko a dandalin Whatsapp

Comments

Popular posts from this blog

Yadda zaka iya amfani da UBA MAGIC BANKING a kyauta

Yadda ake raba Hard Disk na Comuter - Yadda Ake Hard Disk Portitioning

YADDA AKE KIRKIRAR GROUP LINK A DANDALIN WHATSAPP