Yadda ake raba Hard Disk na Comuter - Yadda Ake Hard Disk Portitioning


Yadda ake raba Hard Disk na Comuter - Yadda Ake Hard Disk Portitioning

Assalamu alaikum, Barkan ku da yau sannunku da sake saduwa a wannan dandali na Amarawa Online. Yau cikin yardar Allah zamu kawo kasidar mu akan akan yadda ake raba memory na computerwto disk partitioning
MENENE DISK PARTITIONING?
Disk Portitioningna nufin rarraba ko ince karkasa memory na computer zuwa kashi-kashi. Idan muka lura da kwamfiyutoci na mutane daban daban zamuga wadansu kwamfiyutocin zamuga hard disk din su guda dayane tak, wadansu kuwa kashi kashine Musamman ma ga masu amfani da Laptop, wacce daman sanin kowa ne Hard Disk daya take dauke dashi. Nasan mai tambaya kan iya tambayar cewar to ya akeyi hakan na faruwa? Eh, hakan na faruwa ne sakamako Partition da ake yi ma wannan disk din.Mutane da dama ba susan amfanin Disk partitition ba shiyasa ba su damu da suga sun raba disk din nasu ba, duk da cewar dai yin hakan nada matukar amfani

AMFANIN DISK PARTITION

Hard Disk na computer acikin sa ake ajiye da babbar manhajar sarrafa computer wato computer operating system, shi wannan operating system din, shike da alhakin karba da isar da dukkanin umarnin da mai amfani da computer yake, ya kuma fassara umarnin ga ita comuter. Sannan kuma yanada ma zauni ne acikin hard disk na computer ka a Local disk kenan. Kaga kuwa abu mai muhimmanci kamar wannan bai kamata ace ana chakuda shi da sauran tar kace ba.
  • Idan ya kasance awannan ma ajiyar ka ajiye wani abu mai matsa, wato ace fayel din daka saka aciki yana dauke da kwayar cutar virus, to asaukake zai iya kama operating system na computer ka, daganan dole kaje ayi mata flashing. Kaga kuwa da ace kayi partition na disk din tun afarko da wannan matsalar bata auku ba.
  • Idan yakasan ce hard disk din ba ayi mashi partition ba, kuma ka ajiye abubuwa da adama acikin kwamfiyutar ka, wadanda kake matukar so da kauna, ana cikin hakan kwatsam sai ta samu matsala akeje wajen flashing, kaga dukkanin abubuwan daka ajiye acikin computer ka to kayi asarar su, domin kuwa bazasu dawo ba. Da ace kuwa already drive din naka arabe yake, kuma ka ajiye kayayyakin naka ne acikin dayan ma'ana na biyun to ko bayan anyi Flashing dinne babu wani abu da zai samu kayannanaka. Indai kayi backup
  1. kaje kadanna Start, zakaga ta kawo maka programs din dake cikin computer, sai kawo kasa wajen inda zaka iyayin searching
  2. A cikin filin da zakayi searching, sai karubuta computer amagement sai ka danna Enter
  3. Bayan ya kawo maka sakamako, A bangaren hannunka na hagu za kaga sun wurinda suka rubuta Disk Management sai ka shiga nan
  4. Zakaga ya kawo maka wani akwati acikin sa, akwai bangaroran drive din ka guda biyu, acikin su akwai wani wanda aka rubuta System Reserved to banda shi dayan idan kaje daidai saitin sa sa kayi Right Click
  5. Sai ka shiga inda aka rubuta Shrink Volume
  6. Zai dan dauki lokaci yana Loading karkadamu, idan ya kammala zai nuna maka
  • TOTAL SIZE BEFORE SHRINK MB Anan yana nuna maka adadin girman drive dinka kafin ka mashi partition
  • SIZE AVAILABLE SHRINK SPACE IN MB Nan kuwa sauran filin daya rage maka ne acikin drive dinka,
  • ENTER AMOUNT OF SPACE TO SHRINK IN MB Anan kuwa nan ne zaka saka adadin girman da kake son sabon disk din ka ya dauka, Amma yaka mata ka kaula dacewar dukkanin adadin da zaka saka anan kar ya wuce adadin da yake a available space dinka
  • Dukkani wadan nan abubuwan da suke asama, idan kuka lura zaku ga anyi lissafin sune a megabyte wato MB, kuma dai sanin kowane MB 1000 itake daidai da 1GB wato gigabyte guda daya.
  1. Bayan kasaka adadin girman disk din naka sai ka danna SHRINK zakaga ya fara loading
  2. Da zarar ya kammala loading zai nuna maka Create New Volume sai ka shiga nan
  3. Bayan ya bude sai kayi "RIGHT CLICK" Inda akasa
    (un allocated)
    sai kazabi NEW SIMPLE VOLUME
  • Ka kuma zabar Next
  • Dagan an wani akwatin sako zau bullo
  • Danna NEXT
  • Zabi SIMPLE VOLUME SIZE IN MB
  • Kayi click a zabi na karshe wato kazabi NEXT
  • Zai ce maka Assign the following Drive letter To anan zaka saka kalar sunan da zaka sakawa Drive din na biyu, in kaso kana iya barin sad a D daganan sai ka danna NEXT
  • Sai ka saitashi a NTFS
  • Sai ka danna format in kanason kayi masa formatting
  • Sai ka Danna Next, shikenan An kamala
  • Kasance damu a shafin mu na Facebook

    Comments

    Popular posts from this blog

    Yadda zaka iya amfani da UBA MAGIC BANKING a kyauta

    YADDA AKE KIRKIRAR GROUP LINK A DANDALIN WHATSAPP