Yadda zaka iya amfani da UBA MAGIC BANKING a kyauta
Yadda zaka iya amfani da UBA MAGIC BANKING a kyauta
Assalamu alaikum, Barkan ku da yau sannunku da sake saduwa da wannan blog wato Amarawa Online. A yau kasidar tamu za kawo maku wata hanya ce yadda zaku iya gudanar da harkokin na bankin United Bank for Africa wato UBA da wayar tafi da gidan ka, a kyauta batare da an dauki ko kobo alayin ka na waya ba.
Kasancewar Shekarun baya da suka gabata bankin UBA ya kirko da wani tsari na sa mai suna UBA MAGIC BANKING, wanda yake baiwa masu mu'amala da bankin damar guda nar da harkokin asusun ajiyar su wato Transactions ta hanyar amfani da wayar sa ta salula, batare da yaje wani daga cikin reshen bankin ba, ko zuwa waje ATM machine ba, kawai abun da kake buka wayar hannu komai kankantar ta, layin waya amma ka tabbata layin da kake karbar sakon karta kwana ne wato sms alert daga bankin. sai kayi amfani da USSD CODES da suka samar wato *919#.
Sai ya kasance bankin suna daukar ladar dawainiyar kowane transaction da kayi kamar, checking balance, transfer, da sauran su amma idan katin waya zaka siya zuwa wannan layin naka kyauta ne, layin wayarka bazasu dauki ko sisi ba hakan kuma bankin naka ma ba zasu dauki ko sisi ba. Amma idan wanine zaka sakawa katin, to bankin naka ba zai caje ka kudi ba sai layinka ne zasu dauki mani wasu yan nairori.
Amfanin wannan Dabara
Kamar yadda ya gabata abayanin baya cewa Bankin na ka na daya bullo da wannan tsarin ba shi kadai bane yake da alhakin tafiyar da wannan aikin ba sai sahalewar layin ka na waya da kake amfani da shi, kuma idan baka manta ba munce sai wanda ake maka alert da shi, to kaga kuwa suma layin ba zasuyi aikin banza ba. Dole ne yakasance suna samun dan dari da kobo daga gare ka domin tafiyar da wannnan aiki, hakan ne yasa aduk lokacin da kayi yunkurin bin wannan hanya to dole sai sun dauki kudi alayin naka, TO YAYA ZAN IYA AMFANI DA UBA MAGIC BANKING BATARE DA SUN DAUKI KUDI DAGA LAYI NA BA? YAYA ZAN YI AMFANI DA UBA MAGIC BANKING KODA BABU KUDI ALAYIN WAYA TA?YADDA ZAKA YI TRANSFER NA KUDI, CHECKING BALANCE, DUBA ACCOUNT STATEMENT, PAYING BILL, DA SAURAN SU A UBA ACCOUNT BATARE DA AN DAUKI KO SISI DAGA LAYIN KA BA.
- Ka danna wannan code din,
*919*100000#zasuga kamar zaka siyo kati ne na N100000, ba dole bane sai wannan adadin ba zaka iya sa daga N15,000 zuwa abunda yayi sama. karda dai amount din da zaka sanya ya gaza ma N11,000. - Za su ce maka ka saka lambobin ka na sirri wato PIN karka damu kasaka kawai sai ka tura.
- Daga nan zasu nuna maka cewar adadin kudin daka sanya yayi yawa, saidai ka saka daga N50 har zuwa N10,000. To anzo wurin idan ka duba acan kasa sun rubuta Kadanna Zero 0 domin komawa menu
- Shikenan kawai sai ka yi reply da zero 0 din zaka ga sun kawo ka menu, sai kayi dukkan abun da zakayi batare da layin wayarka sun dauki ko sisin kobo ba ada asusun layin ka ba.

Masha Allah
ReplyDeleteMasha allah
ReplyDelete